Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bayyana cewa ba zata lamunci duk wani yunƙuri na tayar da hankalin jama’a, ko yin abun da zai kawo cikas ga tsaro da zaman lafiya, yayin gudanar da bikin babbar Sallah na shekarar 2026 ba.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu tare da rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargaɗi masu son tada zaune tsaye da cewa duk wanda aka samu da hannu wajen karya doka ko haddasa rikici zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Rundunar ƴan sanda, ta kuma shawarci jama’a da su guji ɗaukar abubuwan da za su iya tayar da hankalin jama’a, tare da kira ga iyaye su kula da ƴaƴansu a lokutan sallar.
Haka kuma rundunar ta gargadi direbobin ababen hawa da su guji tuƙin ganganci, ko yin lodin da ya wuce ƙima, sannan ta buƙaci jama’a su guji yaɗa labaran ƙarya ko kalaman ƙiyayya a kafafen sada zumunta.
Rundunar ta ce, tuni ta kammala dukkanin shirye-shiryen da yakamata, kamar yadda babban Sufeto na ƴan sandan Nijeriya ya bayar, IGP Olatunji Rilwan Disu, da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, don ganin an gudanar da bikin cikin lumana a faɗin jihar.
A ƙarshe, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta taya daukacin al’ummar musulmi murnar babbar sallah, tare da yi musu fatan za a yi bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.
