• Home  
  • Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya ta tsaurara tsaro gabanin Babbar Sallah
- Babban Labari

Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya ta tsaurara tsaro gabanin Babbar Sallah

Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya dake jihar Kano, ta bayyana cewa ta ɗauki tsauraran matakan tsaro, kamar yadda babban sufeton ƴan sadan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayar da umarni, don tabbatar da an gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin kwanciyar hankali da lumana. Mataimakin sufeton ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya, […]

Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya dake jihar Kano, ta bayyana cewa ta ɗauki tsauraran matakan tsaro, kamar yadda babban sufeton ƴan sadan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayar da umarni, don tabbatar da an gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.

Mataimakin sufeton ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya, AIG Garba Ahmed, ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Hussaini, ya rabawa manema labarai ranar talata.

Sanarwar ta buƙaci jama’ar shiyar da suka haɗa da jahohin  Kano da Jigawa, su kasance masu masu bin doka da oda da kuma baiwa jami’an tsaro haɗin kan da yadace don wanzar da zaman lafiya.

Mataimakin sufeton ƴan sandan, ya taya al’ummar musulmin shiyyar murnar bikin babbar sallah ta shekarar 2026.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000