Allah Ya yi wa fitaccen mawaƙin Hausa El’Muaz Birniwa rasuwa a ranar Laraba da yamma sakamakon bugun zuciya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Elmuaz ya rasu ne sakamakon bugun zuciya a lokacin da yake halartar bikin abokin sana’arsa mawaƙi Auta Waziri.
Falalu Dorayi ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa “An je ƙwallo irin ta aure ɗin nan wasu ma sun ce ba a gama ta ba sai ya ce jiri na kwasarsa, daga haka sai ya faɗi. Aka ɗauke shi aka wuce da shi asibiti a nan Kaduna, to bayan kamar awa guda ne asibitin suka ba da sanarwar cewa Allah Ya yi masa rasuwa,”
- Lakurawa Sun Tada Bam A Zamfara- Police
- Wasu masu nazari sun fara ganin gwara jiya da yau a Barcelona aharkar koyarwa.
Elmuaz ya kasance mawaƙi, marubucin waƙoƙi, furodusan fina-finai, kuma shi ne mataimakin ƙungiyar mawaka ta Murya Daya.
Elmuaz na yin waƙoƙin jan-hankali da wa’azantarwa da kuma na siyasa.
Ana sa ran za a yi jana’izarsa a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 1 na rana a Kaduna.