Shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya ce ba a zaɓe su – ƴan majalisa – ba domin su je su riƙa rigima da ɓangaren zartaswa, inda ya ce aikinsu shi ne yin dokokin da za su ciyar da ƙasar gaba.
Akpabio ya bayyana haka ne a tsakuren bidiyon shiri na musamman da aka domin bikin cika shekara biyu na gwmanatin Bola Tinubu.
Da yake magana game da amfanin haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu, ya ce, “idan ka lashe zaɓen majalisa, ko dai ta dattawa ko ta wakilai, waɗanda kake wakilta ba za su ba ka safar hannun dambe ba. Ba dambe muka zo yi ba, mun zo ne domin gudanar da ayyukan da za su ciyar da Najeriya gaba.”
Shugaban majalisar ta nanata cewa akwai alaƙa mai kyau da fahimta tsakanin majalisa da ɓangaren zartaswa a shekara biyu da suke gabata.
“Idan ka ƙarar da lokacinka wajen rikici da ɓangaren zartaswa, waye zai yi wa Najeriya aikin?” in ji shi.