Home » Ma’aikatar Ilimin Nijeriya Ta Kaddamar Da Shirin Kara Inganta Tsaron Makarantu

Ma’aikatar Ilimin Nijeriya Ta Kaddamar Da Shirin Kara Inganta Tsaron Makarantu

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Ma’aikatar Ilimi a Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wani shiri na ƙara inganta tsaro a manyan makarantu, da na sakandare mallakarta da ke ɗaukacin faɗin ƙasar.

Ma’aikatar ilimin ta ce, ta ɗauki matakin ne ganin yadda ake samun ƙaruwar ɗaliban da ke mutuwa a faɗin ƙasar, sakamakon harin ƴanbindiga, ko ƙwacen waya, ko wani rikici da ke haɗawa da su ko ɓarkewar annoba.

Babban sakataren ma’aikatar Ilimi ta Najeriya, Dr Nasiru Sani Gwarzo ya ce za a aiwatar da shirin da aka sake farfaɗo da shi, haɗin gwiwa da ma’aikatar kuɗi da sauran hukumomin tsaron ƙasar don tabbatar da tsare rayuka da lafiyar ɗaliban.

Dr Nasiru Gwarzon ya ce ‘ mun lura da yadda ake fuskantar matsaloli yau da kullum musamman kiyon lafiyar dalibai da rayuwarsu, da harka tsaro, wadda idan aka bar su a hannun jami’o’i ko makarantar sakandare mallakar gwamantin tarayya, su yi gaban kansu, za a iya samun gibi a tsarin da aka samar’ in ji shi.

Har ila yau Dr Gwarzon ya ce, sun zabo shugabannin tsaron makarantu na jami’ai, da shugabanin makarantun sakandare mallakar gwamantin tarayya wajen basu horo na aji da na aikace don ganin sun fahimci sabbin dabarun da za su yi amfani da su wajen kulla da tsaron makarantunsu da lafiyar daliban da suke kula da su.

“Muna da shugabanin makarantun sakandare na gwamantin tarayya su 118, su kuma jami’o’i sun kusa 200, haka kuma muka tara su, su kusan dari uku, muna basu horo, kuma sun koyi abubuwa masu yawa, don tunkarar aikin da ke gabansu” a cewar Dr Nasiru Sani Gwarzon.

Babban sakataren ma’aikatar Ilimi ta Najeriya, Dr Nasiru Sani Gwarzo ya ce ‘ganin yadda yanbindigar ke dauke mana ko halaka dalibai, a wasu lokutan ma halakasu, ko fadan daba ko kwance waya ya rutsa da su, da yadda ake samun barkewar annoba ta kuta a makarantun na daga cikin abin da yasa ma’aikatar ilimi ta kafa sashen don ganin an tunkari matsalar musamman laakari da yadda adadin daliban da ke mutuwa na karauwa,’ a cewarsa.

Ya ce matakin zai yi tasiri wajen ingnata tsaron makarantun da ake da su a kasar.

“Kaga mun toshe gibin da ake da shi na cewar kowacce makaranta tilas sai jami’an tsaro ne za su bayar da shi, wanda kaga dalibai da rawar da zasu taka, akwai wanda su ma hukumomin makaranatun za su bayar, sannan su ma shugabanin tsaron makarantun su ma da wanda su ma za su kawo, kaga dole sai an hada hannu,” in ji Dr Nasiru Sani Gwarzon.

Haka kuma ya ce ba wai iya bita ba, kadai ba, ma’aikatar Ilimi ta kafa wani sabon sashe wanda zai ring kula da tsaron makarantun wanda kuma akwai makamancisa a ma’aikatar kudi ta Najeriya, da bangarorin tsaro wanda kuma zasu yi aiki tare da juna wajen ganin an gudu tare an tsira tare.

Tun a shekara ta 2014 ne dai gwamnatin Najeriya ta ce ta samu taimako na miliyoyin daloli daga gwamnatocin kasashe da dai-dai-kun mutane domin tallafa wa shirinta na samar da tsaro a makarantun da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Cikin kasashen da suka tallafa wa shirin na Safe School Initiative har da Burtaniya wadda ta ba da tallafin Fam miliyan biyu kwatan kwacin Naira miliyan dari biyar.

Sai Norway da ta bayarda dala milyan daya da rabi, da bankin raya kasashen Afrika ya bada dala miliyan daya, yayinda shugaban bankin ya bada gudumuwar dala dubu hamsin.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?