• Home  
  • Ma’aikatar Jin Kai Ta Tarayya Da Jahohi Sun Zamo Matattarar Cin Hanci Da Rashawa — Tsohon Minista
- Babban Labari

Ma’aikatar Jin Kai Ta Tarayya Da Jahohi Sun Zamo Matattarar Cin Hanci Da Rashawa — Tsohon Minista

Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya. Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali. “Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan […]

Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali.

“Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba.

“Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi.

Kazalika ya soki shirin ‘yan siyasa na raba jari ga talakawa, yana mai cewa suna yi ne don boye gazawar gwamnati na samar da abubuwan more rayuwa da damarmaki ga al’ummarsu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai