Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ayyana dokar haramta auren jinsi da luwadi da madigo da sauran dabi’u masu kama da su a kasar.
Kazalika gwamnatin ta kuma ayyana addinin Musulunci a matsayin addini na kasa.
Gwamnatin ta dauki wannan matakai ne a sabuwa dokar tsarin mulkin rikon kwarya ta kasa da babban taron muhawara na kasa da ya gudana ya samar.
Nana Jubi Haruna Maty, tsohuwar ‘yar majalisar dokokin Nijar ce da ta jagoranci fafutuka yaki da wadannan dabi’u a wancen lokaci ta shaida wa BBC irin yadda ta ji dadi bayan gwamnatin ta dauki wannan mataki.
Ta ce,” Gaskiya wannan mataki babban ci gaba ne domin zai kara gyara tarbiyya a tsakanin al’ummar kasarmu.”
Nana Jubi Haruna, ta ce, ” A baya a lokacin da na ke ‘yar majalisa mun yi gwagwarmaya wajen ganin an samar da wannan doka, ga kalubale kala-kala da na fuskanta domin ba barazanar da ba mu fuskanta ba, to amma hakarmu bata cimma ruwa ba, to amma yanzu Alhamdulillah tun da hakarmu ya cimma ruwa.”
Tsohuwar ‘yar majalisar dokokin ta Nijar ta ce yanzu al’adunsu da dabi’unsu za su rika tafiya tare da addini Musulunci, wannan kuma ba karamin abin jin dadi ba ne in ji ta.