Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, Hajiya Maryam Namadi, rasuwa da safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Disamba, 2024.
Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Ya ce, za a yi jana’izarta da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a garin Kafin Hausa.
Gwamnan, da iyalansa sun buƙaci ɗaukacin Musulmi da su yi mata addu’ar samun rahama daga Allah.