Biyo bayan iftila’i na rashin nasarar kwallon kafa da ya afkawa shahafarriyar kungiyar nan ta Manchester City na rashin samun nasara mafi muni tun bayan zuwan mai horas wa Pep Guardiola a ‘yan watannin nan.
Hakan ya sanya kungiyar ta fito da salo kala-kala domin ganin sun dawo kan kadaminsu na nasada kamar yadda suka saba amma abin ya gagari kundila.
Tun bayan zuwan mai horas wa Guardiola kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta zamo gagarabadau a duniyar kwallon kafa.
Sai dai tun watanni uku baya zuwa yanzu sun gamu da mummunar rashin nasara inda a wasanni 12 da kungiyar ta fafata wasa guda daya kacal ta iya lashe wa.
Hakan ya sanya aka tilaatawa ‘yanwasan yin baccin dole a tsaye har na kwanaki biyu a ranakun 24 da kuma 25 ga watan Disamba.
Hakan kuwa ‘yan wasan su kayi suka tsaya a tsaye bayan kammala atisaye suka sha bacci suka more.
Wannan bacci dai sun yishi ne domin dawowa kan kadamin nasara a wannan rana ta kwana daya da bikin Kirsimeti da akewa lakabi da (Boxing Day) inda zasu fafata wasa da Everton.