Danwasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wato Victor Osinhem ya yi rabon kayan abinci na miliyoyin naira ga mabukata.
Ya yi wannan rabon abinci ne kwana daya kafin bikin Kirsimeti a jihar sa ta haihuwa wato Legas.
Osinhem dai ya kasance sanannan danwasa a kasa Najeriya da Afrika dama duniya baki daya a sabgar kwallon kafa inda yake fafata wasansa a nahiyar Turai a kungiyar kwallon kafa ta Galatasary dake kasar Turkiyya.
Wannan abinci dai galibi anfi baiwa iyaye mata inda ya bayyana da bakinsa cewa dukkanin abincin na iyaye mata ne.
Sannan kuma ya rabawa matasa kyautar keke napep domin kowa ya kama sana’a, sai dai kuma ya rabawa iya matasan unguwar da ya taso ne wato Olososun.
Daga karshe ya yi godiya ga al’ummar jihar ta Lagos sannan kuma ya godewa matasan unguwar ta Olusosun.