Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da a ƙirƙiro jihohi guda shida.
Wannan na cikin matsayar da aka cimmawa a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu, wanda mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu suka jagoranta a jihar Legas.
Kwamitin ya tattauna ne kan buƙatu guda 69, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da buƙatar a ƙirƙirar ƙananan hukumomin 278 kamar yadda jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito.
A game da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar a ranar Asabar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi guda shida a duk shiyoyin ƙasar guda shida.
Idan aka amince da ƙirƙirar sababbin jihohi, Najeriya za ta zama tana da jihohi 42 ke nan.