• Home  
  • An Kama Mutane Biyu Da Zargin Safarar Makamai Daga Jigawa Zuwa Katsina
- Babban Labari - Labarai

An Kama Mutane Biyu Da Zargin Safarar Makamai Daga Jigawa Zuwa Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da kama wasu mutum biyu bisa zargin safarar muggan makamai daga jihar Jigawa zuwa Katsina. Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu ya fitar ya ce da asubahin yau ne ƴansandan da ke sintiri tsakanin Ingawa da Karkarku suka kama wata mota ƙirar […]

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da kama wasu mutum biyu bisa zargin safarar muggan makamai daga jihar Jigawa zuwa Katsina.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu ya fitar ya ce da asubahin yau ne ƴansandan da ke sintiri tsakanin Ingawa da Karkarku suka kama wata mota ƙirar Golf maƙare da muggan makamai.

“An kuma kama wasu mutum biyu, mazauna ƙauyen ɓaure da ke ƙaramar hukumar Safana tare da makaman”, in ji sanarwar.

Nasir Mu’azu ya ce binciken ƴansanda ya gano cewa motar ta taso ne daga garin Hadejia da ke jihar Jigawa da nufin zuwa Safana a jihar Katsina.

Makaman da aka kama cikin motar sun haɗa da:

  • Babbar bindiga mai jigida (GPMG)
  • Alburusan bindigar AK-47 1,063
  • Alburusan bindigar PKT 232.

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Karin Naira Biliyan 215.3 A kasafin Kudin 2025

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai