Majalisa Ta Buƙaci Tinubu Ya Dakatar Da Yarjejeniyar Samoa

Majalisar Wakilan Najeriya ta dakatar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu daga aiwatar da yarjejeniyar Samoa da  ta rattaba hannu a kai.

Majalisar ta buƙaci gwamnatin ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar har sai an warware duk wata sarƙaƙiya da ke tattare da yarjejeniyar.

Rahotanni sun bayyana cewa majalisar ta cimma wannan matsaya ne a zamanta yau talata, sakamakon dambarwar da ta dabaibaye yarjejeniyar.

‘Yan Najeriya musamman daga Arewacin Najeriya sun yi wa wannan yarjejeniya tofin Allah tsine, biyo bayan bayanan da suka bayyana cewa akwai wani ƙuduri dake yunkurin kare masu auren jinsi da aikata waɗansu laifuka da suka saɓawa al’ada da addinin su.

Post masu alaƙa

Yan sandan Kano sun gaiyaci Aminu Warkal kan zargin nuna bindiga.

2027: Sama da mutum 10,000 sun nuna goyon bayansu ga Tinubu da Namadi a mazabar Limawa

Gwamnonin Arewa maso Gabas na yin taro a Maiduguri