Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwashe ɗaruruwan ma’aikatanta da iyalansu daga Khartoum da sauran yankunan Sudan, a cewar wani mai magana da yawun Babban Sakataren ƙungiyar.
Antonio Guterres ya yi ta nanata kiraye-kirayen a tsagaita wuta domin barin fararen hula su fice daga yankunan da rikice-rikicen ya shafa.
Mai magana da yawun Babban Sakataren ya ƙara da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ci gaba da aiki da ma’aikatanta da ke ciki da wajen Sudan saboda har yanzu shugaban harkokin diflomasiyyarta, Volker Perthes, yana cikin ƙasar.