Hukumar Kare Hakƙin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya ta sake tunani kan shirinta na kai masu neman mafaka zuwa ƙasar Rwanda.
Kiran na zuwa ne bayan da kotun ɗaukaka kara da ke birnin Landan ta ce matakin haramtacce ne.
Babban kwamishinan hukumar Volker Türk ya ce shirin na Birtaniya ya haifar da damuwa kan dokokin kare ‘yancin bil adama da na ‘yan gudun hijira.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da hukucin kotun, tana mai cewa Birtaniya ta sake duba wasu hanyoyin, ciki har da haɗa hannu da ƙasashen Turai.