Home » Kano: Majalisar Dokoki Ta Tabbatar da Ƙudurin Kafa Masarautu ta 2019

Kano: Majalisar Dokoki Ta Tabbatar da Ƙudurin Kafa Masarautu ta 2019

by Anas Dansalma
0 comment

Majalisar Dokoki Ta Jihar Kano ta Tabbatar da Ƙuduri Kafa Masarautu ta shekarar 2019 da aka yi wa kwaskwarima a matsayin doka a yayin zaman da majalisar a ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Engineer Hamisu Ibrahim Chidari.

Sakataren Yaɗa Labarai na Majalisar, Uba Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan tare da cewa an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da kwamitin gyaran Dokar da mambobin majalisar.

Baya ga wanann majalisar a yayin zamanta na yau, ta karɓi takarda daga mai girma gwamnan Kano bisa buƙatar tantance da tabbatar da naɗin barista Mahmoud Balarabe, a matsayin shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafi da Yaki da Cin Hanci da Rashawa Ta Jihar Kano.

Sannnan gwamnan ya aike da ƙunshin dokar samar da Ma’aikatar Samar da Hanya ga Karkara, da gabatar da taken jihar Kano wacce gwamnatin Kano da haɗin guiwar Jami’ar Bayero Kano ta samar, da Kudirin Dokar Rajistar Filaye ta shekarar 2022 domin majalisar tai nazarinsu da kuma tabbatar da su.

Har’ila yau, majalisar ta karɓi buƙatar gwamnan na tabbatar da Balarabe Hassan Karaye a matsayin cikakken kwamishina na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Jiha da kuma na Hukumar Tallafawa Marasa Lafiya

Majalisar dai ta ɗage zamanta zuwa gobe Laraba bayan da shugaban masu rinjaye kuma mai wakiltar Warawa, Labaran Abdul Madari, ya buƙaci hakan tare da samun goyon bayan Sale Ahmed Marke, mai wakiltar Dawakin Tofa

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi