Home » Majalisar Malamai Ta JIBWIS Ta Tura Malamai Ƙauyuka Domin Karantarwa

Majalisar Malamai Ta JIBWIS Ta Tura Malamai Ƙauyuka Domin Karantarwa

by Anas Dansalma
0 comment

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala na Najeriya Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ta hanyar raya ilimi ne kungoiyoyin addini za su ba da gudunmawa wajen yaki da talauci da miyagun dabi’u.

Shehun malamin na magana ne a taron shekara na gidauniyar raya ilimi da makarantu da kungiyar ta gabatar a Abuja.

Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce tun kafa kungiyar ta dauki matakan kafa makarantu da jan hankalin jama’a wajen muhimmancin neman ilimi don kawar da jahilci da kuma bunkasa zamantakewar alheri tsakanin jama’a.

Malamin ya ce al’umma ba za su shiga halin ni ‘ya su ba matukar ana bin dokokin Allah da kuma hakan ke yin nasara ta hanyar ilimin sanin Allah.

Da ya ke karfafa muhimmancin ayyukan kungiyar na raya ilimi, Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid ya ce kungiyar ta na da makarantu a ko ina a fadin tarayyar Najeriya inda jama’a kawai na bukatar shiga ne don samun karatu.

Mai masaukin baki a taron shugaban majalisar malamai na Abuja Sheikh Ibrahim Duguri, ya ce aikin cibiyar ilimi ta kungiyar da ke Abuja na ci gaba da gudana har sai an kammala aikin ta.

Babban bako a taron tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya ce ba abun da jama’a za su bayar ya zama ya yi kadan ta hanyar gudunmawa ko zuba jari ga raya ilimi.

A yanzu haka JIBWIS ta tura malamai birane da kauyuka har ma da wasu kasashe na Afurka ta yamma don gudanar da tafsirin watan ramadan.   

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?