Majalisar wakilai ta tsoma baki cikin batun zargin da hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a (JAMB) ta yi wa wata daliba mai suna Mmesoma Ejikeme na kirkirar sakamakon bogi wanda hukumar ta shirya na shekarar 2023.
‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda hukumar jarabawar ta gaza nuna dattaku kan lamarin da ya shafi karamar yarinya ta hanyar janye sakamakon jarabawarta tare da dakatar da ita na tsawon shekaru uku.
Inda majalisar ta ce yana yiwuwa akwai hannun wani a cikin wannan lamarin.
Daga nan ne majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da neman hukumar JAMB da ta dakatar da zartar da hukunci har sai majalisar ta kammala bincikenta.
A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar JAMB ta zargi dalibar da kirkirar sakamakon bogi a jarabawar ta bana.