Hukumar karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta ce binciken kwakwaf din da aka gudanar ya nuna bidiyon Dalar da ake zargin tsohon gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje da karbar na goro gaskiya ne.
A shekara ta 2018 ce jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu jerin faya-fayan bidiyo da suka nuna Ganduje yana karbar Dalolin Amurka, abin da aka yi zargin cin hanci ne daga wasu ’yan kwangila.
Sai dai tsohon gwamnan ya sha karyata hakan, inda ya ce hada bidiyon aka yi kawai domin a bata masa suna.
A yayin da yake jawabi wajen wani taron tattaunawa na yini daya kan yaki da rashawa a Jihar Kano a jiya, Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya tabbatar da ingancin bidiyon.