• Home  
  • Majalissar zartarwar Jigawa ta amince da kwangiloli na sama da naira biliyan 91
- Babban Labari - Labarai

Majalissar zartarwar Jigawa ta amince da kwangiloli na sama da naira biliyan 91

Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da bayar da kwangiloli da darajarsu ta haura naira biliyan 91, domin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a sassa daban-daban na jihar. Kwamishinan Lafiya, Dakta Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya bayyana cewa taron majalisar ya gudana ne karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, a ranar 17 ga Disamba, 2025, […]

Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da bayar da kwangiloli da darajarsu ta haura naira biliyan 91, domin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan Lafiya, Dakta Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya bayyana cewa taron majalisar ya gudana ne karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, a ranar 17 ga Disamba, 2025, a matsayin wani bangare na ajandar ci gaban gwamnati.
Majalisar ta amince da ayyukan wutar lantarki ta hasken rana ga asibitoci, jami’o’i da cibiyoyin gwamnati, tare da gina tashar solar mini-grid domin ciyar da muhimman ofisoshi na gwamnati.
Haka kuma, an amince da gina hanyoyin cikin gari, cibiyoyin horo, masallatai, cibiyoyin koyon sana’o’i da gyaran su, domin bunkasa rayuwar al’umma da samar da ayyukan yi.
A ƙarshe, bangaren lafiya da muhalli, majalisar ta amince da gyara asibitoci, samar da kayan aiki, gina magudanan ruwa domin magance ambaliya, da kuma bandakunan jama’a, inda aka jaddada cewa dukkan ayyukan za a aiwatar da su bisa gaskiya da inganci.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai