Majalisun Najeriya Sun Amince da dokar hukunta masu lalata da ɗalibai a Jami'o'i

Majalisun Najeriya Sun Amince da dokar hukunta masu lalata da ɗalibai a Jami’o’i

Majalisar Wakilan Najeriya karo ta 9 ta amince da ƙudirin dokar da zai haramtawa tare da hukunta duk malamin da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a kwalejoji da jami’o’i a ƙasar nan.

Tun a shekarar 2020 Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin mai taken Ba da Kariya da Haramtawa da Hukunta Haike Wa Ɗalibai a Manyan Makarantu wanda ke ɗauke da ƙunshe- ƙunshen hukunci daban-daban.

Shugaban kwamatin Majalisar Dattawa kan harkokin shari’a, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce taron gamayyar ‘yan majalisar ya haɗe kan tanade-tanaden biyu kafin ya gabatar da rahotonsa a zauren Majalisar da aka yi a jiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *