Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda

Makarantar Kurame ta Katsina da ke Malumfashi ta zama zakara gaba ɗaya a gasar wasannin Para-Games ta makarantu karo na farko da Gwamna Dikko Radda ya shirya, wadda aka kammala a Katsina.
Makarantar ta lashe gasar ne bayan ta doke wasu makarantu na musamman guda shida daga sassan jihar da suka halarci gasar.
Ta lashe gasar ne da tarin lambobin yabo guda bakwai na zinariya, bakwai na azurfa da kuma huɗu na tagulla.
Makarantar Makafi da Kurame ta Katsina ta zo ta biyu da lambobin yabo shida na zinariya, takwas na azurfa da tara na tagulla, yayin da Makarantar Al’umma ta Makafi da ke Daura ta zo ta uku.
Da ya ke jawabi a wajen taron, mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin masu buƙata ta musamman, Muhammad Isah-Abba, ya bayyana gasar a matsayin wani babban ci gaba mai muhimmanci.
Ya yabawa gwamnatin jihar Katsina kan shirya gasar, tare da kira ga sauran jihohi da su yi koyi da hakan.
A nasa bangaren, Kwamishinan Wasanni na jihar, Surajo Yazid-Abukur, ya jaddada kudurin gwamnatin Gwamna Radda na bunƙasa harkokin wasanni a kowane mataki.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai