Katsina

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

Rahotanni daga yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da ke Jihar Katsina sun ce jami’an tsaro sun kashe wasu manyan kwamandojin ’yan bindiga biyu a wani artabu da suka yi da ’yan ta’addan da ke ƙarƙashin jagorancin wani da ake kira Kachalla Fulani. Majiyoyi sun ce artabun ya biyo bayan wani harin kwanton ɓauna da ’yan bindigar […]

Read more

Yan Sanda Sun Kama Ɓarayin Wayar Lantarki A Katsina

Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ake zargi da sata tare da lalata kayan gwamnati. Jami’an da ke aiki a rundunar da ke Rimi da suke kan sintirin yau da kullum a ƙaramar hukumar, tare da haɗin gwiwar al’ummar gari ne suka yi nasarar cafke waɗannan mutane uku ɗauke da […]

Read more

Gwamnatin Katsina ta haramta sana’ar POS da cajin waya

Gwamnatin Katsina ta haramta gudanar da sana’ar cirar kuɗi ta PoS da cajin waya da kuma haya da babur a yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da Musawa ta Jihar nan take. Sabuwar dokar zartarwar da Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu ta kuma haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a fadin jihar nan […]

Read more

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka sace a Zamfara

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su tare da kashe ‘ƴan ta’adda’biyar a wasu hare-haren da suka kai a jihohin Zamfara da Katsina. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar 29 ga Mayun 2026. A cewar […]

Read more

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari

Ɗan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya bayyana cewa, ya amsa kiran al’ummar mazaɓarsa ne na tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai. Ya ce, burinsa shi ne ya ɗora kan kishin ƙasa da jajircewar mahaifinsa wajen gina mazaɓarsa, jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya. Yayin da yake jawabi a Daura bayan wani […]

Read more