Majalisar Wakilai za ta ƙada kuri’a a ranakun 10 da 11 ga watan Disamba kan muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ciki har da kirkirar sabbin jihohi da kafa ’yan sandan jihohi.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya sanar da jadawalin a zaman majalisar, inda ya ce tattaunawa kan kudirin sauya kundin tsarin mulki za ta gudana yau da gobe kafin kada kuri’ar mako mai zuwa.
Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan nazarin kundin tsarin mulki, ya bukaci ’yan majalisa su halarci zaman.
Ya shaida wa majalisar kwanan nan cewa kwamitin ya kammala aikin da ake bukata a wannan mataki, kuma yana shirin gabatar da takardun da aka daidaita don a yi la’akari da su.
A farko dai an gabatar da jimillar kudirori 87 da ke neman sauya sassa daban-daban na kundin tsarin mulki.
Kudirorin sun shafi gyaran harkokin zabe da shari’a, ’yan sandan jihohi da batutuwan kudi.
- An Fara Musabakar Alkur’ani Mai Girma Tsakanin Hukumomin Tsaron Kano.
- Gwamnan Kano Abba Kabir Ya ziyarci Yankunan Da Yan Bindiga Ke Yiwa Barazana
Sai dai bayan jin ra’ayin jama’a a matakin jihohi, taron jin ra’ayin jama’a na kasa a Abuja, tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma daidaitawa da kwamitin majalisar dattawa kan kundin tsarin mulki, adadin kudirin da za a kada kuri’a ya ragu zuwa kusan 45.
A ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba, kwamitocin majalisar wakilai da na majalisar dattawa kan gyaran kundin sun gudanar da taron hadin gwiwa da kakakin majalisun jihohi a Abuja yayin da tsarin sauya kundin ya shiga matakin karshe.
