Gwamnatin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE) sun ƙaddamar da shirin horas da malamai 337 kan koyar da harshen Ingilishi a makarantun firamare, Shirin ya shafi makarantu 132 da aka zaɓa, inda ake sa ran ɗalibai sama da 30,000 daga ajin firamare ɗaya zuwa uku za su amfana.
Za a horas da malamai a ƙananan hukumomin Dutse, Gagarawa, Jahun, Kafin Hausa, Malam Madori, Taura da Yankwashi.
Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana shirin a matsayin mataki mai muhimmanci wajen inganta ƙwarewar malamai, ya ce fara koyar da Ingilishi tun daga ƙananan ajujuwa zai taimaka wajen shirya ɗalibai su iya shiga gasa a matakin ƙasa da na duniya.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Shirin PLANE na Ƙasa, Samuel Achimugu, ya ce shirin na samun tallafin Gwamnatin Birtaniya kuma ana gwada shi ne a halin yanzu, idan sakamakon ya yi kyau, za a faɗaɗa shirin a duk faɗin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi da SUBEB.
