Manchester City za ta biya Chelsea sama da fam miliyan 120 don sayen ɗanwasan tsakiyan Argentina Enzo Fernandez idan ta iya ƙulla yarjejeniya kafin rufe kasuwar musayar ƴan wasa. (Telegraph – subscription required)
Chelsea ta sanya farashin kusan fam miliyan 100 kan ɗanwasan gefen Portugal Pedro Neto, mai shekara 26, wanda ake rade-radin cewa ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya za ta ɗauke shi. (Mail)
Manchester City da Arsenal da kuma Tottenham suna zawarcin Neto, wanda ya koma Chelsea kan fam miliyan 54 daga Wolves a 2024. (Metro)
An bai wa Manchester United damar sayen dan wasan tsakiyan Sifaniya Marc Casado, mai shekara 22, wanda Barcelona ta sanya a kasuwa. (Sport – in Spanish)
Duk da rashin son sayar da shi da Manchester United ta nuna, Galatasaray ta yi wa ɗanwasan tsakiyar Portugal Bruno Fernandes tayin albashin fam miliyan 18.3 a kowace kakar wasa – ninki biyu na albashinsa na yanzu, a wani mataki na neman shawo kanshi ya bar Old Trafford. (Telegraph)

