Daga: Muhammad Inuwa Ibrahim
Majalisar Masarautar Hadejia a jihar Jigawa ta mika sakon jaje da ta’aziyarta ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon matsalar tsaron da ta haifar da kisan gilla a yan kwanakin nan.
Da yake jawabi a wani taron hadin gwiwa da al’umomin yankin da abin ya faru Galadiman Hadejia, Alhaji Usman Abdul’aziz, ne ya bayyana hakan.
Ya yi Addur Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya bai wa yan uwansu hakuri da juriyar rashin da aka yi.
Taron dai na da nufin tattauna hanyoyin da za a bi don kawo karshen matsalar tsaron, inda ya jaddada cewa harkar tsaro aiki ne na hadin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro da kuma mahukunta.
- Wike Ya Kwace Filin Sakatariyar PDP A Abuja
- Hisbah Ta Kama Ummin Mama, Kan Zargin Ta Da Yada Bidiyon Tsaraicin Ta A TikTok
Sannan ya yi kira ga shugabannin gargajiya, iyaye da duk masu ruwa da tsaki da su hada kai domin kawo mafita.
Kazalika, Alhaji Usman Abdul’aziz ya tunatar da Hakimai da su sake kafa kwamitin dattijai mai mutane ‘goma-goma’ a kowanne yanki don lura da harkokin tsaro da ci gaban yankunansu.
Tun da farko, Hakimin Waje, Katukan Hadejia, Alhaji Iliyasu Ibrahim, ya gabatar da shugabannin yankunan da suka hada da dagatai da ‘yan kwamitin dattijai daga unguwannin NTA, Shagari, Warwarin, Bello Bayi da kuma Mandara.

