• Home  
  • Tinubu Ya Sanya Dokar Ta-baci A Jihar Ribas
- Babban Labari

Tinubu Ya Sanya Dokar Ta-baci A Jihar Ribas

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna da mataimakinsa da daukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da ayyana dokar ta-baci a Jihar. Tinubu ya kuma ayyana Navy Vice Marshal Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin Gwamnan Rikon Jihar Ribas, a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya game da harin da aka kai wa bututun […]

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamna da mataimakinsa da daukacin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ribas, tare da ayyana dokar ta-baci a Jihar.

Tinubu ya kuma ayyana Navy Vice Marshal Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin Gwamnan Rikon Jihar Ribas, a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya game da harin da aka kai wa bututun man fetur a Jihar.

“Ina amfani da tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya wajen ayyana dokar ta-baci da kuma dakatar da gwamnan da mataimakinsa da zabbabbun ’yan majalisar na tsawon wata shida, daga yau 18 ga watan Maris, 2025” in ji shugaban kasan.

 

Ya sanar da hakan ne jim kadan bayan shan ruwa a ranar Talata, ’yan sa’o’i bayan wani zaman gaggawa da ya yi da manyan hafsoshin tsaro a sakamakon harin da ’yan ta’adda suka kai kan bututun mai na Trans-Niger Pipeline (TNP) da ke yankin Bodo da ke Karamar Hukumar Gokana ta Jihar Ribas.

Mahara sun kai harin ne bayan barazanar yin hakan da suka bayar a makon jiya a sakamakon kara tsanani da rikicin shugaban jihar ya yi tsakanin ’yan majalisar da kuma gwamna Simi Fubara.

Ibok-Ete Ibas shi ne tsohon Babban Hafsan Sojin Ruwa na Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2021 a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai