• Home  
  • Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Murabus
- Babban Labari

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Murabus

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi murabus daga muƙaminsa. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar Kwankwasiyya ta fitar, wadda kakakinta Dr Habibu Sale Mohammed ya fitar da yammacin ranar Juma’a. Ya ce mataimakin gwamnan ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da tabbatar […]

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi murabus daga muƙaminsa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar Kwankwasiyya ta fitar, wadda kakakinta Dr Habibu Sale Mohammed ya fitar da yammacin ranar Juma’a.

Ya ce mataimakin gwamnan ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da tabbatar da ba a haifar da tsaiko a mulkin jihar ba.

“Sai dai ya kamata a fahimci cewa ajiye aikin da ya yi, ba ya nufin ya amince da tuhume-tuhumen da majalisar dokokin jihar ke masa. Mataimakin gwamnan yana nan da gaskiyarsa. Kawai ya yi murabus ne domin fifita Kano da al’ummarta da kuma hana duk wani abu da zai iya barazana ga cigaban jihar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa tsohon mataimakin gwamnan zai mayar da hankali ne wajen raya ƙungiyar Kwankwasiyya musamman domin fuskantar zaɓukan 2027.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai