Home » Matan da ke gabatar da shirin ‘Mata A Yau’ sun ziyarci hukumar Hisbah

Matan da ke gabatar da shirin ‘Mata A Yau’ sun ziyarci hukumar Hisbah

by Anas Dansalma
0 comment
Matan da ke gabatar da shirin 'Mata A Yau' sun ziyarci hukumar Hisbah

Matan da ke gabatar da shirin ‘Mata A Yau’ a wani gidan talabijin a nan Kano, sun ziyarci shugaban hukumar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan wasu kalaman da suka yi, a cikin shirin dangane da batun gaisuwa tsakanin mata da miji.

A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin ‘Mata A Yau’ na Facebook, an ga ɗaya daga cikin matan na cewa, idan mace ba ta gaida  mijinta ba,  shi sai ya gaisheta, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara.

Malamai da dama a ciki da wajen birnin Kano, sun yi martani mai zafi, haka nan ma masu amfani da kafafen sada zumunta musamman ma Facebook a Arewacin Najeriya, sun caccaki masu gabatar da shirin inda mafi yawa ke ganin hakan na iya haifar da rigingimu tsakanin ma’aurata.

A yayin ziyarar da suka kai wa babban kwamandan na Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, matan sun bayyana cewa kuskure aka samu, amma ba saƙon da suke son isarwa ke nan ba,

kuma sun bayyana cewa hankalinsu ya tashi sosai kan yadda jama’a suka taso musu, sannan suka nemi al’ummar Musulmi ta yi haƙuri saboda kalaman nasu da suka ɓata musu rai.   

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi