Home » Za mu inganta harkokin yawon bude ido a Najeriya ~ Misis Lola Ade-John

Za mu inganta harkokin yawon bude ido a Najeriya ~ Misis Lola Ade-John

by Hassan Abdu Mai Bulawus
0 comment
Za mu inganta harkokin yawon bude ido a Najeriya ~ Misis Lola Ade-John

Sabuwar ministar ma’aikatar yawon bude ido, Misis Lola Ade-John, ta ce za ta yi aiki tare da ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki don mayar da bangaren yawon bude ido ya zama babban hanyar samun kudaden shiga ga Nijeriya.

Ade-John ta bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawarta da gidan rediyon Nijeriya a Abuja jim kadan bayan kama aiki a ma’aikatarta.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rahoto cewa Ade-John ta samu tarba daga babbar sakatariyar ma’aikatar yada labarai da al’adu, Dr Ngozi Onwudiwe da shugabannin hukumomi da sassan ma’aikatar.

Ministar, ta ce yawon bude ido ya kunshi kasuwanci da hada kai da masu ruwa da tsaki, inda ta sake jaddada cewa, za ta hada kai da masu zuba jari, da gwamnatoci, da jama’ar gari domin inganta fannin.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi