Daga: Hauwa Umar Tela
A cikin wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar, ya ce an daidaita farashin ne sakamakon samun ci gaba mai kyau a bangaren makamashi na duniya da kuma raguwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Matakin da matatar man Dangote ta dauka na nuna irin jajircewarta na yin daidai da hakikanin kasuwancin makamashi a Najeriya da sauran kasashen duniya wanda hakan ya samo asali daga hawa da sauka da farashin ke yi a kasuwa.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in kula da sa hannun jari da sadarwa na matatar Dangote Anthony Chiejina ya fitar, kamfanin ya bayyana cewa wannan sabon mataki ya biyo bayan irin wanda aka dauka a ranar 19 ga watan Janairun 2025 Inda aka kara farashin litar man bayan farashin danyan man fetur ya tashi a kasuwar duniya.
- Yadda Aka Dakatar Da Sheikh Bin Uthman Daga Limancin Masjid Sahaba
- Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Cigaba Da Taimakon Nakasassu
Matatar man fetur din ta Dangote ta nemi abokan hultarta da su kiyaye da ragin domin na kasa su amfana.
A karshen shekarar 2024 matatar man fetur din ta Dangote tayi hadin guiwa da gidan man fetur na MRS domin samun saukin farashi yadda ya kamata idan kamfanin ya rage litar mai.