Daga:Mujahid Wada Musa
Masallacin Jami’ur Rahman, wanda a da ake kira da Masjid Sahaba, ya dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga limanci biyo bayan hudubar da ya yi a ranar 24 ga watan Janairu.
Asalin masallacin, wanda Bin Uthman ke jagoranta tsawon shekaru 24, na kusa da sabon wanda AY Maikifi ya sayi filin.
Bayan Maikifi ya samu mallakar filin a hannun gwamnati don gina sabon masallacin Sahaba, sai ya tuntubi Bin Uthman inda suka amince da cewa tsohon masallacin Sahaba zai dawo sabon gini.
Sai dai kuma a yayin huɗubar da ya yi a ranar 24 ga watan Janairu, wacce ta haifar cece-ku-ce, Bin Uthman ya ba da labarin yadda aka rage masa matsayi wajen gudanar da harkokin masallacin.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Cigaba Da Taimakon Nakasassu
- HISBA Ta Kama Matasan Da Suka Daurawa Kansu Aure
A cewar sa, an nada shugabanni uku masallacin amma ba a nada shi a jagora ba.
Daily Nigerian ta gano cewa huɗubar ta ranar 24 ga watan Janairu ta fusata masallata, inda suka kusa dukan sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Abdulkadir Isawa.