Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Mai magana da yawun ‘yan sandan Najeriya a Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce wannan shirin na inganta insharar motoci zai tabbatar da cewa masu motoci masu bin tituna sun sami kariya.
‘yan sandan ya ce aiwatar da dokar, wanda aka fara a Legas a ranar Asabar, na bin umarnin Sufeto-Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, wanda ya bukaci a tabbatar da cewa duk masu ababen hawa sun mallaki inshorar motocin mai inganci.
- Matatar Dangote Ta Rage Farashin Litar Man Fetur
- Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Cigaba Da Taimakon Nakasassu
Ya bukaci direbobi da masu ababen hawa su bi doka da oda, yana mai cewa wadanda suka saba za a hukunta su.
Mai magana da yawun ‘yan sanda ya kuma bukaci jami’an da ke aiwatar da dokar su nuna kwarewa a yayin gudanar da aikinsu.