Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa ta ACF, ta nuna damuwarta kan yadda matsalar rashin tsaro ke neman kassara yankin Arewacin Najeriya, Shugaban Kwamitin Amintattun ƙungiyar Alhaji Bashir Muhhamd Ɗalhatu Wazirin Dutse ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da ƙungiyar takai jihar Borno.
Alhaji Bashir Ɗalhatu ya ƙara da cewa yanayin yadda ake samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankin na Arewa abun tsoro ne.
ACF ta nemi mahukunta da su ɗauki matakan gaggawa da zasu kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ya addabi yankin.
Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ita ce babbar barazana da take addabar yankin. Musamman Jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina.
- Ku Miƙa Wuya Ko Ku Ɗanɗana Kuɗar Ku- Gargaɗin Tinubu Ga Ƴanbaindiga
- Taron KILAF Zai Hada Jama’a Daga Kasashe 66 A Kano
A baya baya ne dai Ƙungiyar ta dattawan Arewa ta gudanar da wani taro a Kaduna inda aka haɗa kan manyan Arewacin Najeriya domin nemo bakin zare da mafita ga yankin.