Home » Ministan Sufurin Jiragen saman Najeriya ya ba da umarnin rufe filin jirgin Murtala Muhammad

Ministan Sufurin Jiragen saman Najeriya ya ba da umarnin rufe filin jirgin Murtala Muhammad

by Anas Dansalma
0 comment
Keyamo

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayar da umarnin rufe sashen saukar jirage na kasa da kasa a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas daga ranar 1 ga watan Oktoban shekarar nan ta 2023.

Ministan, wanda ya sanar da hakan yayin wata ziyarar da ya kai filin jirgin saman na Legas ya ce za a rufe filin ne domin a samu damar yin wasu gyare-gyare.
Ministan ya kai ziyarar ce tare da rakiyar shugaban Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), Kabir Yusuf Mohammed.
Hakan na zuwa ne bayan da Ministan ya sanar da soke jinginar da filayen jiragen saman Legas da na Malam Aminu Kano da ke nan jahar Kano, wanda gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi.
Ya kuma dakatar da ci gaba da aikin kafa kamfanin jiragen sama mallakin Najeriya na Nigeria Air, har sai abin da hali ya yi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi