Home » Wata mata ta roki kotu ta raba aurenta

Wata mata ta roki kotu ta raba aurenta

by Anas Dansalma
0 comment
Mata

Wata matar aure mai suna Ruqayya Mukhtar ta garzaya kotun Shari’a dake Rigasa a jihar Kaduna inda ta nemi a raba aurenta da mijinta Nasiru Hamza saboda ƙaurace mata da ya yi.

Ruqayya ta ce ba za ta ci gaba da zama da Hamza ba saboda ya ƙaurace mata na tsawon shekaru biyu, bayan haka kuma Rukayya ta ce yana jibgar ta haka kawai idan ya bushi iska.

Amma Hamza ya ƙaryata duk abin da Ruqayya ta faɗa, yace yana ƙoƙari matuƙa wajen kula da matarsa.

Hamza ya ƙara yin bayanin cewa saboda tsananin nema domin ciyar da iyalinsa, wata rana sai da daddare ya ke koma wa gida a gajiye, amma duk da haka yace yana ƙoƙari wajen biya mata buƙata, kuma yace tun da ya auri Ruqayya bai taɓa dukan ta ba kuma bai taɓa zaginta ba.

Alƙalin kotun Anass Khalifa ya tambayi Ruqayya ko tana da shaidar da za ta iya gabatarwa, tace tana da ita.Saboda haka sai Aƙali Anass Khalifa ya ɗage shari’ar zuwa ranar 5 ga watan nan na Satumba domin Ruqayya ta gabatar da shaidarta a zaman da kotun za ta yi a ranar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi