Mota Ta Yi Ajalin Mutane 5 A Kasuwar Soro Jihar Bauchi

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Wani mummunan hatsarin mota ya faru a garin Soro da ke Karamar Hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi, inda wata mota ta shiga kasuwa ta markade mutane biyar suka mutu ta Kuma kade wasu da dama suka samu manyan raunuka.

Rahotanni daga dake fitowa daga garin sun bayyana cewa hatsarin ya auku ne da safiyar jiya Juma’a inda aka tabbatar da cewa mutane biyar sun rasa rayukansu a nan take.

Ana zargin direban motar da yin ganganci ko rashin kulawa yayin tuki, lamarin da ya janyo wannan matsala wacce hakan ya Sha faruwa saboda yawanci ana gudanar da harkokin kasuwanci ne a bakin hanya.

A yayin hatsarin, wasu mutane da dama sun samu raunuka daban-daban, kuma an garzaya da su zuwa asibiti mafi kusa domin samun agajin gaggawa.

An bayyana cewa jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya sun isa wurin da hatsarin ya faru don daukar matakan da suka dace, amma har zuwa wannan lokacin babu wata sanarwa daga rundunar ‘yan sanda ko hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC.

Al’ummar Soro na ci gaba da jimamin wannan mummunan hatsari da ya janyo ajalin wasunsu, tare da alhini da kuma addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasu, sannan ya ba wa wadanda suka jikkata lafiya.

 

Post masu alaƙa

Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika

Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari