Home » MUHASA Ta Ɗauki Nauyin Horar Da ‘Yan Kannywwood 12 Dabarun Aiki

MUHASA Ta Ɗauki Nauyin Horar Da ‘Yan Kannywwood 12 Dabarun Aiki

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Tashar Talabijin da Radio ta MUHASA da ke yaɗa shirye-shirye a 92.3fm da kuma ta startimes lamba 170 ta ɗauki nauyin jarumai da masu shirya finafinai a Masana’antar Kannywwood har 12 sabbin dabarun aiki. 

Mamallakin tashoshin Alhaji Muhammad Babandede OFR ne ya biya wa jaruman da masu shirya finafinan domin ƙara musu ƙwarewa a fagen sana’ar su.

Horon ya gudana a bikin baje kolin fina-finan harsunan Afrika da tallata su da aka gudanar a tsangayar koyon ilimin da sadarwa na jami’ar Bayero ta Kano.

An kwashe kwana biyar ana gudanar da abubbuwa iri daban-daban da suka shafi fasahar shirya finafinai da kasuwancinsu.

Alhaji Abdulkarim Muhammad da ke shirya baje kolin da ake kira da KILAF ya bayyana godiyarsa ga mamallakin tashoshin MUHASA TV da Rediyo Muhammad Babandede OFR.

Ya ce, “Babu wani mutum guda da ya yi irin abin da Alhaji Muhammad Babandede ya yi, kuma wannan ya nuna irin kishin al’ummarsa da ya ke yi”.

Alhaji Abdulkarim Muhammad, ya yi kira ga manyan Malaman Arewacin Najeriya da ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su daure su fahimci abin da ake nufi da Film, kuma su bashi gudunmawar da yake buƙata domin ingantanshi yadda zai yi daidai dai tsarin addinimu da al’adar mutanen Arewa.

“Film fa zamani ne, babu wanda zai iya hana shi, dan haka ya kamata a zo a haɗa hannu domin ingantanshi ta yadda zai yi daidai da addinin mu da al’adar mu”

A ƙarshe Mas’ud Umar ɗaya daga da ya wakilici waɗanda suka ci gajiyar tallafin ya bayyana godiyarsa da jin daɗinsa ga Alhaji Muhammad Babandede OFR.

Ya ce, “Muna miƙa cikakkiyar godiyarmu ga Alhaji Muhammad Babandede OFR bisa wannan tagomashi, ba za mu bashi kunya ba, za mu yi abin da ya dace”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?