Wani ƙwararren likitan cutar sukari, Dokta Mansur Ramalan, ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 14 ne ke fama da ciwon ciwon suga.
Dokta Mansur ya bayyana hakan ne da yake jawabi yayin wani taron tantancewa da wayar da kan jama’a kan kamuwa da ciwon sukari da kungiyar wayar da kan al’umma akan ciwon sukari tare da hadin gwiwar gidauniyar Gatefield ta shirya wa mazauna babban birnin tarayya Abuja a karshen mako.
Yayi taron, an buƙaci gwamnati ta dawo da haraji kan lemun kwalba mai zaƙi, ta kuma riƙa saka abin da aka tara wurin samar da magani kyauta ga masu ciwon sukari.
- ICPC Za Ta Bibiyi Ayyuka 60 Da Suka Laƙume Miliyan Dubu 21 A Kaduna
- Ciyaman Ɗin Kabo Ya Saya Wa ‘Yan Gabasawa Filin Maƙabarta
Dokta Mansur ya ce: “Akwai harajin da gwamnatin da ta shude ta amince da shi akan kayan ruwa mai zaƙi, amma an daina cire kudaden a watan Fabrairun wannan shekara.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya ta dawo da wannan haraji. Idan ta dawo da shi, muna son ta yi amfani da abin da aka tara domin yi wa masu ciwon sukari magani kyauta.
“Masu ciwon sukari na cikin wahala sosai saboda magungunan suna da tsada sosai.”
Ramalan ya ce kusan kashi shida cikin 100 al’ummar Najeriya na da ciwon suga, ya kara da cewa: “Idan ka yi hasashen ga jimillar al’ummarmu kusan miliyan 230 zuwa miliyan 240, muna aƙalla mutane miliyan 12 zuwa 14 na fama da ciwon suga.”
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar hadin gwiwar rage cutar sukari ta kasa, Benard Enyia, wanda ke fama da ciwon sukari nau’i na 2, ya ce farashin maganin ciwon sukari ya yi yawa sosai, yana mai kira ga gwamnati ta taimaka.