Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sanya sabuwar ranar aikin kidaya da yiwa gidaje rijista
Hukumar kidayar jama’a ta kasa ta tabbatar da cewa nan bada jimawa ba shugaba Bola Ahmad Tinubu zai sanar da sabuwar ranar da za a gudanar da aikin kidaya da yiwa gidaje rijista na 2023.
Shugaban hukumar Alhaji Nasiru Kwarra ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya gana da shugaban kasa a fadar sa dake birnin Abuja.