Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun samu nasarar ceto mutane 24 da aka yi garkuwa da su a Kabugu Lamba da ke karamar hukumar Maru ta jahar Zamfara.
Wata majiya ta shaida mana cewa, sojojin sun samu wani rahotannin sirri ne kan maboyar ‘yan ta’addan da ke dajin, inda aka tsare da wadanda akayi garkuwa da su.
Sojijin sun ce, bayan samun labarin ne suka dauki matakan gaggawa wajen kai hari wurin, inda aka yi musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da dakarun sojojin na tsawon lokaci, wanda ya sa ‘yan bindigar gudu suka bar wadanda suka yi garkuwa da su a cikin wasu gine-gine.
A arangamar, sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 24 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ‘yan bindiga hudu, ya yin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
A yayin gudanar da bincike, wadanda aka yi garkuwa da su, sun bayyana cewa wasu daga cikin su sun shafe kwanaki 21 zuwa 53, a hannun masu garkuwa da su.