• Home  
  • Muna Iya Ƙoƙarinmu Wurin Kare Al’ummar Arewa– Sarkin Hausawan Owerri
- Babban Labari - Labarai

Muna Iya Ƙoƙarinmu Wurin Kare Al’ummar Arewa– Sarkin Hausawan Owerri

Mai Martaba Sarkin Hausawan Owerri jihar Imo kuma Sakataren Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohin kudu maso kudancin Najeriya Alhaji Auwal Baba Sa’idu Sulaiman ya bayyana abin da su ke yi wa al’umar Hausawa da ke yankin

Mai Martaba Sarkin Hausawan Owerri jihar Imo kuma Sakataren Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohin kudu maso kudancin Najeriya Alhaji Auwal Baba Sa’idu Sulaiman ya bayyana cewa a matsayin su na shuwagabanni kuma jagororin al’umma, suna yin dukkan mai yiyuwa wurin ganin sun kare al’ummar hausawa dake zaune a Jihar ta Imo.

Sarkin ya bayyan wa tashar MUHASA irin ƙoƙarin da fadarsa ke yi wurin inganta rayuwar al’ummar  Hausawan da ke rayuwa a yankin, ya kuma kara da cewa masarautar tana da ƙungiyoyi daban-daban wadanda aikin su shine su tabbatar da zaman lafiya da bin doka tsakanin al’ummar Hausawa da sauran ƙabilu dake zaune a yankin.

“Muna iya bakin ƙoƙarin mu don ganin mun tsare wa mutanen Arewa mutuncin su da dukiyoyin su,”

Ya kuma yi kira ga mutanen Arewa dake zaune a Jihar Imo da su zamo masu bin doka, ya kuma ya bayyana farin cikin sa kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin kiyaye duk wata matsala da ka iya tasowa tsaknin su da abokan zaman su.

Hausawa daga yankin Arewacin Najeiya suna fita fatauci sassa daban-dabn na Najeriya don fatauci., saidai akan yi rashin sa’a wasu lokutan su fuskanci tsangwama da cin zarafi daga al’ummar yankin da suka je, wanda hakan yake haifar da rashin jituwa da kuma asarar dukiya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai