Home » Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 8,034 A Cikin Watanni 11

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 8,034 A Cikin Watanni 11

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Rundunar Sojin Nijeriya ta sake aika karin sojoji zuwa Filato domin kwantar da tarzoma

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce sojoji sun hallaka jimillar ‘yan ta’adda 8,034, sun kama wasu da ake zargi 11,623 yayin da kuma suka kuɓutar da mutane 6,376 da aka yi garkuwa da su daga watan Janairu zuwa Disamba 2024. 

Daraktan yaɗa labaran harkokin tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis a Abuja.

Daraktan ya ce, tun farkon wannan shekara sojojin sun fuskanci barazana daban-daban a yankuna guda biyar da ke fama da matsalar tsaro a faɗin Najeriya.

Ya ce sojojin sun yi amfani da ƙwarewa wurin kare kasar daga barazanar ta’addanci da rashin tsaro.

Manjo Janar Edward Buba ya ce baya ga mutanen da suka kuɓutar, dakarun soji sun ƙwato makamai 8,216, alburusai 211,459.

 

Ya ce dakarunsu sun hana ɓarayin mai satar da aka ƙiyasta cewa ba domin jajurcewarsu ba da an sace abin da ya kai na sama da Naira biliyan 57 a cikin watanni 11 da suka gabata.

“Abubbuwan da muka ƙwato sun haɗa da bindigogi kirar AK47 guda 4,053, bindigu na gida guda 1,123, bindigogin Danish 731 da kuma ƙananan bindigogi 240.

“Bugu da kari, sojoji sun kwato lita miliyan 53.1 na danyen mai da aka sata”

Daraktan ya ƙara da cewa, a yankin Kudu maso Gabas, dakarun Operation UDO KA sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 666, sun kuma kama wasu 893 da ake zargi, yayinda suka kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su har 323. Kamar yadda kamfanin Dillacin Labaran Najeriya NAN ya bayyana.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?