Mutane 3 sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Najeriya

An tabbatar da mutuwar mutum uku a wani hatsarin jirgin ƙasa a Najeriya, inda kusan mutum 40 suka jikkata.

Kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen ƙasan Najeriya, NRC ta tabbatar, lamarin ya faru ne a jiya Litnin kuma fasinjoji da dama sun samu raunuka.

Rahotanni sun ce jirgin ƙasa ya sauka daga kan layinsa ne a hanyar Warri zuwa Itakpe cikin yankin Agbor na jihar Delta a kudancin ƙasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce tuni ta tura jami’an kai ɗaukin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa zuwa wurin da taragan jirgin suka sauka domin ba da taimakon da ya wajaba.

Sai dai ana fargabar adadin waɗanda suka mutu ya haura uku, kamar yadda wasu ganau suka bayyana

Shugaban ƙaramar hukumar Ika North-East Mr. Monday Odigwe, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa sama da fasinjoji 35 sun jikkata, inda ake ci gaba da duba su a asibiti.

Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori ya yi jaje ga waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Post masu alaƙa

Zulum ya bai wa sojoji kyautar motocin yaƙi, ya tallafa wa ’yan gudun hijira

Yan bindiga sun lafta wa manoma sabbin haraji a Sakkwato

Wasu Tsiraru Ne Ke Rura Matsalar Tsaro A Najeriya — Christopher Musa