Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse.
Ya ce hatsarin ya afku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi, 16 ga Nuwamba 2025, a ƙauyen Jigawan Kurma da ke kan titin Kiyawa zuwa Azaren Jihar Bauchi.
- Babban Hafsan Sojin Nijeriya Ya Umarci Dakarunsa Su Kubutar Da Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi.
- An Kama Masu Kaiwa Yan Bindiga Man Fetur A Nijar
A cewar SP Shiisu, “Mota kirar Hummer ce da ta taso daga Kano zuwa Potiskum ɗauke da fasinjoji 18. Hatsarin ya faru ne bayan fashewar tayoyi biyu, sakamakon gudun wuce sa’a da direban yake yi.”
Ya ƙara da cewa sauran 11 da suka samu munanan raunuka an garzaya da su babban asibitin Birnin Dutse, inda aka sallami huɗu daga cikinsu bayan samun kulawa.
