Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Waidi Shaibu ya umurci dakarun operation Fansan Yamma su ƙara kaimi a ƙoƙarinsu na kuɓutar da ɗaliban da aka yi garkuwa da su daga makarantar sakadire ta ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi.
Da ya ke yi wa dakarun jawabi a lokacin da ya kai ziyara jihar, babban hafsan sojan ya buƙace su su yi amfani da bayanan sirrin da suke samu yadda ya kamata wajen gudanar da ayyukansu, kuma su ci gaba da farautar ƴan bindigar ba dare ba rana ba tare da gajiyawa ba.
- An Kama Masu Kaiwa Yan Bindiga Man Fetur A Nijar
- Afrika Ta Kudu Ta Zargi Isra’ila Da Yunkurin Share Falasdinawa Daga Kasarsu.
Cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Operation Fansan Yamma Captain David Adewusi ya fitar, ya kuma ce Janar Shaibu ya gana da jam’ian sa kai da masu farauta, inda ya bayyana su a matsayin abokanan aiki masu muhimmanci.
Ya kuma buƙace su da su yi amfani da ilimin su na sannin lungu da saƙo na yankin tare da haɗin gwiwar sojojin domin gano tare da hallaka ƴan bindigar.
”Wajibi ne mu ceto yaran nan, ku yi aiki bisa ƙwarewa kan bayanan da za ku samu, wajibi ne a yi nasara.” a cewar shi.

