Sakamakon fari da tashe-tashen hankula da aka dade ana fama da a Somaliya, daruruwan mutane ne suka fake a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Mogadishu, babban birnin kasar.
Nur Shekh Isak, jami’in sansanin ‘yan gudun hijira na Gunsoor da ke Mogadishu, ya yi nuni da cewa fari ya yi mummunan tasiri ga rayuwar mutane.
Isak ya ba da bayanin cewa iyalai 500 ne suka nemi mafaka a sansanin a cikin makonni biyu da suka gabata kuma mutanen da ke sansanonin na bukatar agajin jin kai.
Da yake lura da cewa ‘yan gudun hijirar da ke sansanonin na zama a gidajen da aka yi da buhuna da yadi, Isak ya jaddada cewa hare-haren Kungiyar Ta’adda ta Al-Shabaab da kuma fari na haifar da hijira.
Yawancin ‘yan gudun hijirar da ke sansanin yara ne.