Mutane kusan 80,000 sun rasa matsugunansu a jihar Filato

Akalla mutane 80,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin watanni uku sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, kamar yadda wani jami’in yankin ya ce, yayin da sojoji ke kara karfafa tsaro domin kawo karshen rikicin.

Tun a watan Mayun da ya gabata ne jihar Filato ta fuskanci yawaitar hare-hare a tsakanin Musulmai makiyaya da kuma al’ummar Kiristoci manoma, a rikicin da karamar hukumar ta ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 300.

  Ko da yake Babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja, ya ziyarci Mangu da ke jihar Filato a ranar Asabar domin fara gudanar da ayyuka na musamman don kawo karshen rikicin.

Gundumar Mangu na daya daga cikin wuraren da rikicin baya-bayan nan ya barke inda aka yi ta sace-sace a kauyuka tare da lalata filayen noma.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr