A cigaba da dambarwa game da sahihancin bidiyon dala da ake zargin tsohon gwamnan jihar Kano da karɓa,
Gandujen ya ayyana sammacin da aka aike masa na bayyana a gaban hukumar Karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa a matsayin siyasa.
Wannan kalamai sun fito ta hannun tsohon kwamishinan Labarai da Ayyuka na cikin gida Muhammad Garba wanda ya ce wannan ba komai ba ne face bita da kulli domin taɗe Ganduje.
Ya kuma ce wani salo ne na siyasa mai cike da hassada domin suna hasashen Ganduje zai samu matsayi a gwamnatin tarayya wanda hakan zai ba shi damar ba da gagarumar gudunmuwa ga al’ummar jihar Kano.
Haka ita jam’iyyar APC a nan jihar Kano ta shawarci tsohon gwamnan, Ganduje, da ya kauce wa batun bayyana a gaban hukumar, inda jma’iyyar suka bayyana hakan a matsayin siyasa da kuma ƙoƙarin zubar masa da ƙima.
Abin jira dai a gani shi ne yadda gwamnan zai amsa kiran hukumar ko kuma akasin haka bayan da shugaban hukumar Muhyi ya tabbatar da sahihancin bidiyon karɓar dalar da ake zargin na cin hanci ne.